Wakoki

 

 

Wakokin da Aminu Ladan Abubakar (ALA) Ya Rera Don Girmamawa ga Emiratus da Farfesoshi

Aminu Ladan Abubakar (ALA), shahararren mawaki kuma marubucin Hausa, ya yi suna wajen amfani da fasaharsa don girmama manyan mutane da suka taka rawar gani wajen cigaban al’umma. A cikin wadannan wakokin, ya bayyana halaye, dabi’u, da jajircewar fitattun Emiratus da Farfesoshi na Nijeriya, wadanda suka yi fice wajen bunkasa ilimi, gudanar da bincike, da kuma ayyukan raya al’umma.

Sunayen Fitattun Mutane da ALA ya Girmama a wadannan wakoki. A latsa kowanne suna domin saukar da wakar ko saurare.

  1. Dr. Hauwa Bugaji
      

    Fitacciyar malama mai kishin adabi kuma ta bayar da gudummawa wajen bunkasa karatun mata a Nijeriya.
  2. Emiretus, Farfesa Abdulkadir Dangambo

    Babban masani a fannin harsunan Hausa da al’adun gargajiya, wanda ya yi aiki tukuru wajen bunkasa harshe da rubuce-rubuce.
  3. Emiretus, Farfesa Abdulkadir Dangambo 2
  4. Emiretus, Farfesa Dandatti Abdulkadir
    Masanin tarihi wanda ya shafe shekaru yana bincike da koyarwa don fahimtar asalin al’adun gargajiya a Nijeriya.
  5. Farfesa Abdalla Uba Adamu
     Hazikin malami wanda yake rike da mukamin Farfesa guda biyu a fannonin ilimi da fasahar na'ura mai kwakwalwa.
  6.  Farfesa Yusuf Muhammad Adamu
    Masanin kimiyar kasa kuma mahaddaci, wanda ya taka rawar gani wajen gudanar da bincike kan cigaban adabi da kimiyyar muhalli.
  7. Farfesa Ahmadu Bello Zaria
    Fitaccen malami mai kwarewa a fannin arulin waka, wanda ya tallafa wa nazarin rubutattun wakoki.
  8. Farfesa Ahmadu Bello Zaria 2
  9. Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza
    Masanin adabi da kuma marubuci wanda ya yi fice wajen rubutun adabin Hausa na zamani.

  10. Farfesa Aliyu Muhammad Bunza 2
  11. Farfesa Ango Abdullahi
    Jagora da mai bada shawara, wanda ya kasance mashahuri a harkokin shugabanci da cigaban ilimi.
  12. Farfesa Gaji Fatima Tata
    Malama wadda ta ba da wajen kishin bunkasa ilimin mata da karatun jami'a.
  13. Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi
    Masani a fannin kimiyyar adabin Hausa, wanda ya bada gudummawa wajen bunkasa ayyukan adabi.
  14. Farfesa Isa Mukhtar
    Masanin kimiyyar harshe wanda ya taka rawar gani wajen nazarin kagaggun labarai da adabi
  15. Farfesa Jibril Aminu
    Fitaccen masanin lafiya kuma tsohon minista, tsohon sanata kuma jakadan Nijeriya wanda ya bada gudummawa wajen kyautata harkokin lafiya a Nijeriya.
  16. Farfesa Magaji Tsoho Yakawada
    Masani a fannin rubutu da adabin Hausa
  17. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau
    Masani mai fadi da hangen nesa a fannin ilimin addini da adabi da kuma shugabanci
  18. Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau 2 
  19. Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau 3
  20. Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau 4 
  21. Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
    Jagora a fannin ilimin kimiyyar walwalar harshe da fassara.
  22. Farfesa Salisu Ahmad Yakasai 2

 

 


2 Comments